SHAREDDireban shugaba Buhari ya rasu

Muhammadu Buhari

Direban shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu bayan doguwar jinya a asibitin fadar gwamnati da ke Abuja.

Direban mai mukamin “Master Warrant Officer”, Sa’idu Afaka ya jima kwance a asibitin kafin ya rasu a wannan Talatar.

Wata sanarwa da kakakin fadar ya fitar, Garba Shehu na cewa shugaban na cikin alhini kuma ya miƙa ta’aziya da iyalai da ƴan uwan direban nasa.

Direban ya rasu ne adaidai lokacin da shugaba Buhari ya tafi birnin London domin duba lafiyarsa.

Marigayi Afaka ɗan Kaduna ne wanda aka bayyana a matsayin mai rikon amana da ƙwarewa a fanin aikinsa.

Direban ya kafa tarihi da shan yabo a shekara ta 2016, lokacin da ya tsinci damin kuɗin ƙetare yana tsaka da aikin hajji a Saudiyya, kuma ya miƙawa hukumar alhazai ta Najeriya domin cigiyar mai kuɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here