Dillalan Abinci Sun Amince Da Cigaba Da Kai ka Ya Kudancin Nijeriya.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugabannin dillalan Shanu da na Abinci a karkashin kungiyar Amalgamated Union of Foodstuff da Cattle Dealers of Nigeria (AUFCDN) sun amince da kawo karshen killace kayayyakin zuwa kudu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sun cimma wannan matsaya ne a wata ganawa da ke gudana tare da wasu gwamnoni a Abuja a yau Laraba.

Abdullahi Tom, wani shugaban matasa na dillalan shanu a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi yana cikin shugabannin da suka yi kira a gare su da su kawo karshen yajin aikin masana’antar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here