DIKKO RADDA A CIKIN ‘YAN GUDUN HIJIRA SHEKARAR 2018…..

  Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Ƙananan Hukumomi Ƙanƙara, Safana, Danmusa, Batsari, da Jibiya sune suka fi fama da matsalar rashin tsaro, tun a shekarun baya, inda ‘yangudun hijira suka yawaita har a cikin birnin Katsina, a wancan lokacin.

A shekarar dubu biyu da goma sha takwas (2018) Shugaban hukumar ƙanana da matsakaitan masana’antu ta Najeriya, wato Small and Medium Enterprises Development Agency of Nigeria (SMEDAN) a takaice ya shiga cikin ‘yan gudun hijira, inda ya kai ɗauki na tallafin Hatsi da kayan abinci iri daban-daban a wadannan yankunan.

A ranar Asabar ta takwas ga watan Satumba  Shekarar dubu biyu da sha tara 8/9/2019 Dakta Dikko Umaru Raɗɗa ya kaddamar da wani shiri na bayar da tallafi ga wadanda Ibtila’in’yan bindiga ya Afkawa a garin Batsari a Fadar Sarkin Ruma. Inda ya bada Tallafin Al’kama buhu ɗari, Masara buhu ɗari, wake buhu Ashirin da biyar da Gero.

Kananan hukumomin Dan-musa da Safana ma suna daya daga cikin, masu fama da rashin kwanciyar hankali da ya sabbaba masu masu kaura daga gidajen su zuwa inda zasu samu mafaka, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa a nan ma ya shiga tsamo-tsamo a cikin su da kayan Masarufi, inda Raɗɗa ya raba Buhunnan kayan abinci Iri daban-daban ko wannensu buhu saba’in 70 a ko wace karamar hukuma.

Akwai sauran kananan hukumomi shida da Dakta Dikko Umaru Raɗɗa ya raba Nau’ikan kayan abinci buhu arba’in-arba’in 40 a ko wace karamar hukuma.

Haka kuma a karamar hukumar Katsina, inda a nan ma ‘yan gudun hijira suka samu tallafin.

Fiye da Naira Miliyan huɗu ne Raɗɗa ya kashe a wadannan ayyuka na jin kai ga ‘yan gudun hijira, a shekarar ta dubu biyu da sha tara.

Dakta Dikko Umaru Raɗɗa Shine Shugaban hukumar tallafawa Kanana da matsakaitan masana’antu ta Najeriya wato (SMEDAN) kuma mai neman takarar Kujerar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin Inuwar Jam’iyyar APC a shekarar dubu biyu da ashirin da ukku. 2023

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here