Advert
Home Sashen Hausa DAURIN AUREN FUNTUA;  WA AKA YI WA IHU DA MIYAGUN KALAMAI?

DAURIN AUREN FUNTUA;  WA AKA YI WA IHU DA MIYAGUN KALAMAI?

 

Sabo Ahmad Funtua

@Katsina City News

An yi wa wadanda suka halarci daurin aure gidan Sallau Arawa da aka yi a ranar Asabar din da ta gabata 28/8/2021 a layin Dan Ammani kusa da gidan Sulumka Funtua, ihu da miyagun kalamai.

Sallau Arawa, wanda wani jigon ne jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Dandume ta Kudu, ya aurar da ‘ya’yansa guda biyu; Zainab da Farida a ranar.

Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya isa wajen daurin auren lafiya, inda ya samu kyakkyawar tarba daga mutane Funtua da ‘yan daurin auren.

Bayan ya isa wajen da wasu mintuna sai ga tawagar Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa da Shugaban jam’iyya na riko, Malam Shittu S. Shittu sun iso.

Isowar su wajen sai wasu matasa da dattawa suka rude da ihu ba ma yi! Ba ma yi!! Da wasu kalamai marasa dadi, wasu ma ba za a iya buga su a jarida ba.

Da kyar da ban magana mutanen suka tsahirta.

An yi ta ba matasan nan magana da kyar aka shawo kansu suka janye niyyarsu ta yi wa wani babban dan siyasa da ake zargin ‘yana takarar Gwamna zindir, tare da dan rakiyarsa.

Matasan sun bar wajen daurin auren suka tattaru inda aka yi niyyar cin abinci da niyyar nan za su kammala manufarsu.

Gwamna ana kammala daurin auren ya bar Funtua zuwa Kafur, inda ya yi Sallar Azahar da La’asar, ya kuma yi gaisuwa rashin wani yaronsa da aka yi. Daga nan ya je ya yi zumunci.

Ganin abin da ya faru, ana gama daurin auren duk wani babba sai ya yi ta kansa, amma duk wanda ya zo fita ba mai ce masa kala, sai ma jinjina in ban da tawagar Mustafa Inuwa, wadda sai da aka rika ba ta kariya da ban magana.

 

Daga baya wasu gungun matasa sun rika yawo cikin Funtua suna fadin ba ma yi! Suna kiran sunan wani dan takara.

Katsina City News

@www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

@www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@www.thelinksnews.com

07043777779.08137777245

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Likitocin ƙwaƙwalwa da dama na barin Nijeriya, Malamin jami’a ya yi gargaɗi

Farfesa ilimin ƙwaƙwalwa, Farfesa Taiwo Sheikh ya ce ɓangaren likitocin ƙwaƙwalwa shi ne ya fi samun naƙasu a ɓangaren ƙarancin likitoci da ke faruwa...

Gwamnatin Kano ta rufe makarantar da a ka binne Hanifah

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta rufe makarantar da a ka binne Hanifah Gwamnatin Nijar Kano ta bada umarnin rufe Noble Kids Academy, makarantar kuɗi da ke...

Kwazo Tunani da Hangen nesa yasa mukaga dacewar ya zama Gwamnan jihar Katsina.  -Alliance for Democracy and Purposeful Leadership- ga Sanata Sadiq Yar’Adua

Kwazo Tunani da Hangen nesa yasa mukaga dacewar ya zama Gwamnan jihar Katsina.  -Alliance for Democracy and Purposeful Leadership- ga Sanata Sadiq Yar'Adua A ranar...

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari a wani Sansanin Soji dake Shimfiɗa, ƙaramar Hukumar Jibiya ta jihar Katsina

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Sansanin Soji A Katsina ’Yan bindiga sun kashe wani soja da wani jami’in Rundunar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC)...

PHOTO NEWS: President Muhammadu Buhari(GCFR ),has commissioned the newly remodelled Murtala Muhammad Square

President Muhammadu Buhari(GCFR ),has commissioned the newly remodelled Murtala Muhammad Square. #PMBinKaduna #KadunaUrbanRenewal