Advert
Home Sashen Hausa Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware...

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware yankin kudu

Dattawan arewa sun nemi gwamnati ta amince da bukatar kudu maso gabas a raba ta da Najeriya Wannan na zuwa ne ta hannun wasu dattijai da suka shigar da batun kotu don neman maslaha A bangare guda, wasu lauyoyin kudu sun amince da hakan, sun bayyana goyon baya da jama’ar ta kudu.

Wata tawagar dattawa daga Arewacin Najeriya ta nemi babban kotun tarayya reshen Abuja da a roki ‘yan majalisu a Najeriya su cire yankin kudu maso gabas daga Najeriya kafin aiwatar da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin Najeriya. Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’I, Abdul-Aziz Sulaiman da Aminu Adam sun shigar da batun kotu tare da bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen rage faruwar rikice-rikice da zubar da jinane a daga ‘yan awaren yankin. Sun yi ikirarin cewa ba sa son a maimaita yakin basasar da aka yi a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970 wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyoyin Naira, Daily Sun ta ruwaito.

Wadanda ake magana akansu a cikin karar sun hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF), Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki ta Kasa.

Sai dai a wani martani na gaggawa, lauyoyin yankin kudu maso gabas masu magana da harshen Igbo a Najeriya sun nemi kotu ta hada su a jerin wadanda ake magana a kansu. Lauyoyin da ke karkashin wani Babban Lauyan Najeriya, Cif Chuks Muoma, Ukpai Ukairo, Ebere Uzoatu da Hon Obi Emuka suna neman kotu ta ba su izinin shiga karar a matsayin wakilan al’ummar yankin Kudu maso Gabas. Sun shigar da wannan batu a ranar Litinin ta hannun Victor Onweremadu ya shigar, inda suka bayyana cewa, bukatar dattawan Arewan ya dace da bukatarsu, Premium Times ta ruwaito. Dangane da wannan bukata, kotu a karkashin mai shari’a Inyang Eden Ekwo ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba domin caccaka tsinke akai.

Yankin kudu ya jima yana fama da hare-haren ‘yan IPOB, wata haramtacciyar kungiyar aware da ke fafutukar kafa kasar Biafra.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021 Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of...