Darajar Bitcoin ta faɗi yayin da China ta haramta amfani da shi

Bitcoin

Farashin kuɗin intanet na Bitcoin ya yi ƙasa da dala 34,000 a karon farko cikin wata uku bayan China ta sanya dokokin haramci kan masu amfani da kuɗaɗen intanet ɗin wato cryptocurrency.

A jiya Talata ne China ta hana cibiyoyin kuɗi da kamfanoni yin mu’amala da masu hada-hada da kuɗin intanet.

Haka nan ta gargaɗi masu zuba jari game da mu’amala da su a ɓoye.

Wannan ya biyo bayan faɗuwar da kuɗin ya yi a makon da ya gabata da kashi 10 cikin 100 bayan kamfanin ƙera motoci na Tesla ya ce ya daina karɓar kuɗin na Bitcoin.

Zuwa ranar Litinin, darajar kuɗin ta faɗi da kashi 22 cikin 100, faɗuwar da ta kai kusan dala 6,000 a cikin awa 24.

A gefe guda kuma, kuɗaɗen Ethereum da Dogecoin sun yi faɗuwar kashi 25 da 29 cikin 100 kowannensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here