Ɗan sanda ya harbe mutum biyar a Jihar Enugu

'Yan sandan Najeriya

‘Yan sandan Jihar Enugu sun tabbatar da mutuwar mutum biyar bayan wani ɗan sanda ya kai wa wani gida hari a birnin Enugu ranar Lahadi.

Kazalika, ‘yan sandan sun ce wasu mutum huɗu sun ji mummunan rauni kuma suna samun kulawa a asibiti.

Kwamishinan ‘yan Sanda Mohammed Aliyu ya tabbatar da faruwar tsautsayin, yana mai umartar mataimakinsa da ya ƙaddamar da cikakken bincike. Ya ce tuni an kama ɗan sandan da ake zargi da aikata kisan.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, inda ɗan sandan wanda ke aiki tare da wani kamfani ya fita tare da kai wa wani gini hari a unguwar Golf Estate da misalin ƙarfe 9:30 na safe.

Kwamishinan ya bayar da umarnin a gaggauta kammala binciken domin ɗaukar mataki na gaba.

Ba kasafai ake samun jami’an tsaron Najeriya da aikata irin wannann harbe-harben ba a bainar jama’a duk da cewa ya zuwa yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa ya ɗan sandan ya kai harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here