Advert
Home Sashen Hausa Dangote Bai Sha’awar Sayar Mana Hannun Jarin Matatar Mai – Shugaban NNPC

Dangote Bai Sha’awar Sayar Mana Hannun Jarin Matatar Mai – Shugaban NNPC

Babban Daraktan Kamfanin Mai na kasa watau NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce Aliko Dangote bai so ya saida musu da hannun jarin matatar da yake gina wa a garin Legas.

Mele Kolo Kyari ya ce ya na da kyau kamfanin NNPC ya zuba hannun jari a kamfanin na Dangote, saboda gwamnati ta samu ta-cewa a matatar da ake gina wa.

An ruwaito cewa shugaban NNPC din ya ce kamfanin na NNPC ya yi burin sayen kashi 20% na hannun jarin da kamfanin attajirin ‘dan kasuwan ya mallaka a garin Legas.

“Babu kasar da za ta zura idanu a rika irin wannan kasuwanci, wanda ya shafi harkar mai, wanda yake da hadari. Sai ka tsaya kurum ka na kallo”

“An ba mu dama, amma ban tabbatar ko Aliko Dangote zai so ya saida hannun jarinsa a kamfanin ba. Zan iya cewa mu ne mu ka kawo maganar saida hannun jarin, bai so ya saida na shi hannun a matatar.”

Mele Kyari ya ce NNPC za ta sa hannu a harkar kasuwancin taki, mai, gas da kananan matatun danyen mai, domin fadada inda gwamnatin tarayya ta shiga.

“Ba na tunanin Dangote zai yi murna sosai da wannan. Za mu dauki kashi 20% na kamfanin tace mansa, akwai hanyar da za a bi ayi wa kamfaninsa daraja a kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

VICTIMS OF KIDNAPPINGS IN BATSARI REGAIN FREEDOM AFTER 66 DAYS IN CAPTIVITY.

From Misbahu Batsari. Some of the victims of kidnappings were this Friday 23-07-2021 release from captivity in Batsari after spending 66 days in the hands...

Just In: Plane Crash Lands In Kwara, Passengers Evacuated

Many passengers, including some highly placed Nigerians, narrowly escaped death after an aircraft belonging to one of the major airlines crashed upon landing in...

Yar’Adua: I’ll Resist Attempt to Impose Guber Candidate on Katsina Citizens

Francis Sardauna in Katsina A chieftain of the ruling All Progressives Congress (APC) in Katsina State, Senator Abubakar Sadiq Yar’Adua, yesterday vowed to resist any...

Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta

DAGA IRO MAMMAN “Allah ka saka min. Allah abin da su ke min ka yi musu, ka yi wa yaran su, iyayen su, ‘yan’uwan su....
%d bloggers like this: