Daya daga cikin masu neman Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Katsina a zaben Shekarar 2023 Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya sayi tikitin neman takarar.

Dan Majalissar Tarayya mai Wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada Alhaji Abubakar Yahaya Kusada ne ya Sayi form din a madadadin Dangiwa wanda a halin yanzu yana Kasa mai Tsarki wurin gudanar da Ibadar Umrah.

Dangiwa wanda Tsohon Shugaban Bankin Bada Lamunin Ginin Gidaje ne na Gwamnatin Tarayya, yana daya daga cikin masu neman takarar Gwamnan da ake ganin suna samun goyon baya daga al’ummar Jihar Katsina.

Wane Fata Kuke Mashi?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here