Advert
Home Sashen Hausa Dan shekara 71 ya mutu yayin da yake tarawa da Karuwa

Dan shekara 71 ya mutu yayin da yake tarawa da Karuwa

Wani magidanci dan shekaru 71 ya mutu a lokacin da yake tsaka da tarawa da wata karuwa a dakin otal. Lamarin ya auku ne a kauyen Ogijo a yankin karamar hukumar Sagamu ta jihar Ogun a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Mutumin da aka bayyana sunansa da Ajibola Olufemi, bayanai sun nuna cewar yaje otal din ne domin ya samu ya huta, anan ne ya hadu da wata karuwa, inda suke tsaka da tarawa da juna, mutumin ya fado inda ya mutu nan take. A cewar mai kula da otal din.

Bayan an sanar da ‘yan sanda abinda ya faru, suka dauke gawar mutumin zuwa mutuware dake Sagamu inda aka aje gawar mutumin, haka kuma, an gano katinsa na cirar kudi tare da lasisin tukin mota a dakin otal din. Tuni aka sanar da iyalan mutumin abinda ya auku.

Inda su kuma jami’an tsaro suka yi awon gaba da karuwar domin fadada bincike. A lokacin da manema labarai suka tuntubi kakakin rundunar’yan sanda na jihar Ogin Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar wannan lamari, yace suna kan bincike domin gano musabbabin mutuwar mutumin.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...