Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki…

Tsohon shugaban kwalejin ma’aikatan bankin Najeriya (CIBN), Prof Segun Ajibola, ya bayyana cewa mutane su daina ruduwa da fadin darajar Naira idan aka danganata ga Dalar Amurka.

Segun ya bayyana cewa da N500, dan Najeriya zai ci ya koshi a yau.

Farfesan wanda Malamin ilmin tattalin arziki ne a jami’ar Babcock, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 22 ga Satumba, yayin hira a tashar NTA.

A cewarsa, darajar kudi na nuni ga karfin tattalin arzikin kasa da kuma rauninsa.

Yace: “Har yanzu Naira na da karfin Da N500, dan Najeriya zai iya ciyar da kansa a yau amma idan muka danganata a Dalar Amurka ko Fam, babu abinda zaka iya yi da Fam daya a Landan, ba zaka iya sayan wani abun kirki da Dala daya ba a New York (Amurka).”

– Hausa Trust News

– 24/09/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here