Dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar Katsina, Hon. Salisu Iro Isansi, ya aza harsashin ginin wasu manya-manyan aiyuka a karamar hukumar sa…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City Newsy

A ranar Lahadi 21/11/2021 ne Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina, ya dora harsashin wasu manya, kuma muhimman ayyuka a karamar hukumar Katsina.  Ayyukan sun hada da gina makarantar firamare, a Unguwar Malali dake yankin Tudun ‘yanlifida, da gina Azuzuwan karatu, a cikin makarantar Makafi dake kofar ‘yandaka, kan hanyar Batsari, da gina Titi da ya taso daga Mobil zuwa Shatale-talen Kofar ‘yandaka, da wani Titin da ya taso daga  kofar Durbi,zai hade da kofar Marusa.

Da yake jawabi a wajen aza harsashin aikin, Hon. Salisu Iro Isansi yace wannan yana daga cikin Al’kawari da ya dauka tun a yakin neman zabe, kuma bai manta ba, inda yace, amfara aikin, wanda ba zai dakata ba sai an kammalasu duka.

Al’umar yankin Unguwar Malali da na Tudun ‘yanlifida sun nuna farinci, inda sukai ta san barka da samar da wannan Makaranta ta Firamare wadda sukace, ba karamin ci gaba bane, duba da yanda yaransu suke tafiyar kilo mitoci kafin su isa inda suke karatu a yanzu. Sun roki Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Aminu Bello Masari, da a saka sunan Alhaji Iro Isansi Model Primary, domin tunawa da Mahaifin Danmajalisar.

Daga cikin wadanda suka samu halartar bikin aza harsashi ginin akwai Gwamnan Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari, da    ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi, na jiha Farfesa Badamasi Lawal, sai Mataimakin Gwamnan Katsina da yasamu wakilcin mai baiwa Gwamnan katsina shawara a akan sha’anin Noma, Alhaji Sabo Musa, SSA Restoration, Wakilin Magajin Garin Katsina, Da sauran manyan baki, wanda dukkaninnsu, sunyi son barka akan wannan gagarimin cigaba da Danmajalisar ya kawo a yankunan da yake wakilta.

wakilan Katsina City News sun zaga da tawagar Danmajalisar zuwa shiyyoyin da aka ƙaddamar da ayyukan inda ta ganewa idonta, gami da jin ra’ayoyin jama’a, akan wannan aiki, inda aka fara da Unguwar Malali, Makarantar Makafi, zuwa Titin Kofar Durbi, kofar Marusa, dakuma Mobil, Rafin dadi, zuwa inda ya tuƙe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here