Hon. Sada Soli Jibia Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaita da Jibia ya samar da Makarantun a garin Magama dake cikin karamar hukumar Jibia da kuma garin Yandaki dake cikin karamar hukumar Kaita.

An gina Makarantun da dakin karatu guda biyu masu dauke da azuzuwan karatu guda shidda hade da kujerun zama da tebura, da kuma allon rubutu na zamani.

Bugu da kari kuma Dan Majalisar ya samar da ruwan sha a Makarantun, inda ya assasa gina rijiya da somer aka sanya tankuna da na’urar wutar dake jawo ruwan mai amfani da hasken rana, tare da kawunan famfuna, yadda Daliban zasu samu ruwa cikin sauki.

Samar da Makarantun da Dan Majalisar ya yi taimaka ma kokarin Gwamnatin Jihar Katsina ne, a kokarinta na inganta harkar ilmi a Jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here