DAN MAJALISA YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA-BAYA A BATSARI.

 

Misbahu batsari @ Katsina City News

Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar Hukumar Batsari ta jihar Katsina, Alhaji Jabiru Yusuf Yau-yau, ya sha da kyar
a daren jiya lahadi da misalin karfe 7:30pm na dare.

Wasu gungun mahara dauke da miyagun makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne domin karbar kudin fansa suka killace garin Garwa dake cikin yankin karamar hukumar ta Batsari. A dai-dai lokacin kuma dan majalisar yana cikin garin, ya je ne wajen wata ta’aziyya tare da iyalan shi.

Wani ganau ya bayyana mana cewa sun shigar da dan majalisar wani gida inda suka bashi wasu kaya ya canza domin badda bami, sannan suka fita da shi ta baya suka tsere.

Su kuma ‘yan bindiga sun bi gida-gida suna neman shi har ma sun yi ma mutanen garin barazanar cewa idan basu fiddo shi ba, za su yaba wa aya zaki.

Daga bisani dai sun harbi motar shi da ya bari a garin sannan sun sace awaki, tumaki da shanu.

Daman dai lamarin tsaro a yankin na Batsari abun kullum kwam gaba kwam baya yake domin ta kai ga wasu kauyukan ma ‘yan bindiga sun karbe ragamar gudanar da ikon su dama sauran al’amurransu baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here