..kawai ana fakewa da hukumar kwastam, an siyasantar da ita saboda babu kamfanin da aka taba yi wa haka, Cewar Muhammadu Maslaha

…an baiwa kamfanin damar ya je ya biya duti, tsawon shekara biyu cikin motoci sittin ya biya na mota hudu kadai, Cewar Kwanturolan Kwastam Na Katsina

Kimanin shekaru biyu kenan da rufe kamfanin sayar da motoci mallakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina malam Shitu Shuaibu Shitu da hukumar kwastam ta yi, dake kan titin Ibrahim Badamasi Babangida dake cikin garin Katsina.

A daren jiya ne, da misalin karfe daya da rabi na daren jiya litinin jami’an hukumar kwastam suka dira kamfanin inda suka kwashe motoci guda ashirin suka kai su helkwatar hukumar dake Katsina.

Da yake Karin bayani ga yan jarida da safiyar yau Talata, kan samamen da hukumar kwastam suka kaiwa kamfanin a daren jiya, manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Muhammadu Shitu ya ce ina son in bayyana maku abinda ya faru da wannanan kamfani namu na Maslaha Motors, saboda tsantsagwaron rashin adalci ne aka shiryawa wannan kamfani, ba don komai sai dan ana tunanin shi shugabanta, shi ne shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina kuma kamfani ba na shi ba ne shi kadai a fake da guzuma a harbi karsana.

Muhammadu Maslaha ya kara da cewa kamar shekaru biyu da suka wuce, mun samu bakuncin jami’an kwastam da jami’an sojoji dauke da makamai, sun mamaye kamfanin tun karfe shidda na safe. A matsayina na jami’in gudanarwa na wannan kamfani na zo wurin domin tattaunawa da shugaban da aka turo domin gudanar da aikin, Lawal Aliyu Tito Safana, inda ya jagoranci rufe wannan kamfani tare da daukar motoci guda takwas a wancan lokacin. Bayan sun dauki wadanan motocin jim kadan y ace zai sake dawo wa, domin maigidansa y ace ya zo ya karo motoci, wadanda ya diba ba su is aba, saboda an ba su labarin a Maslaha Motors akwai motoci sama da guda dari, daga nan sai aka rufe kamfanin, su ka kawo takardu aka lillika a kamfanin. Kuma sun daukar mana motoci bisa zargin bas u da Duty, wanda wannan ba gaskiya bane sun nemi Duty kuma mun kai masu shi, sai suka ce ba masu kyau ba ne, muka ce a ba mu dama, mu biya Duty motoci arba’in , kusan sau talatin ina zuwa Abuja, sai daga aka fitar da jaddawali kuma yana da kura-kurai da dama.

Mun tabbattar da siyasantar da hukumar kwastam aka yi, saboda a tarihin kamfanonin sayar da motoci a Najeriya ba’a taba samun kamfanin da hukumar kwastam ta yi wa irin wannan cin zarafi ba. Daga baya aka sake fiddo mana jadawalin za mu biya naira milyan saba’in da hudu, muka je muka fara biyan miliyan goma har aka ba mu motoci guda hudu.
A daren jiya da suka kawo wannan samame sun kwashe mana motoci akalla guda ashirin na miliyoyin daruruwa, duk da cewa ba mu kin biyan Duty ba, alhalin sune ba su ba mu damar biyan dutin ba. Shekarar mu biyu gam da rufe mana kamfani.

Muhammadu ya ci gaba da cewa tun daga shugaban na kasa Kanal Hameed Ali har zuwa PSO na shi Birgediya Janar Isah Buhari sun siyasantar da gidan Kwastam, saboda wani ra’ayi na su ko na wasu yan siyasa, ba zargi bane abu da ya tabbata, muna kwararan hujjoji, an taba neman mu bada cin hanci a gidan Sule Yari anan Katsina, muka ki badawa saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari y ace a daina cin hanci da rashawa. Har ila yau, shugaban hukumar kwastam ta kasa yana da hannu dumu-dumu cikin siyasar Katsina saboda yana tare da su a Abuja, kuma shugaban kasa Buhari na kallo ana zaluntar mu ya ki sanya baki ko ma ya sanya bai amfana mana da komai ba, an zalunce mu ana wulakantar da mu har kwana tara na yi a hannun su.

Da yake jawabi dangane da samamen da jami’an hukumar kwastam suka kai a daren jiya litinin a kamfanin Maslaha Motors, mukkadashin kwanturola kwastam Alhaji Dalha Wada Chedi ya bayyana cewa wannan samame an kai shi a wannan kamfanin sayar da motoci na Maslaha Motors dake nan Katsina sakamakon umurni da muka samu daga helkwatar mu dake Abuja, na lalle aje kamfanin Maslaha Motors dake karkashin kulawarmu watau Seal a dauko motocin nan.

Alhaji Dalha Wada Chedi ya kara da cewa ina son mutane su sani abun ya faro shekara biyu da suka wuce watau ranar 25 ga Yuli 2019. A wannan rana da muka je motoci guda sittin ne muka samu a kamfanin, bisa zargin cewa ba su biya kwastam Duty ba, sai aka sanya aka rufe su, aka dauko guda takwas aka kawo su nan gidan Kwastam aka ajiye. Duk da haka mai girma shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa, Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya yi namijin kokari na ba shi wata dama ga shi mai Maslaha Motors na cewa ka zo ka biya hukumar kwastam akan motocin nan guda sittin kuma daga can helkwatarmu aka rubuto adadin kudin da ya kamata ya biya, a maimaikon ya biya jimlar wadannan motoci guda sittin,sai ya biya na motoci biyu kacal yau shekara biyu fa kenan da bashi wannan damar amma mota biyu kadai ya biya mawa.

Alhaji Wada Chedi ya ci gaba da cewa duk da wannan alfarma da hukumar kwastam ta yi wa Maslaha Motors, duk da mun rufe kamfanin, sai da ya sanya aka zare motoci ashirin da bakwai (27) daga cikin hamsin da biyu da suka rage. A dokar kwastam idan ka dauke wani abu dake karkashin kulawar kwastam, to ka saba doka ta 164, to doka ta hau kanka watau Customs Management ACT 2004. Wannan doka ta baiwa jami’an kwastam dama duk lokacin da aka samu zargi mai karfi ta bada damar akai samame a kowane lokaci ko da rana ko tsakar dare, jami’an kwastam na iya zuwa, wannan dokar kasa ta ba mu wannan damar.

Har ila yau, a sashe na 147 na wannan kundi y ace duk wasu kaya da aka shigo da su a Najeriya ta karkatacciyar hanya , wannan kayan hukunci a kama su a kuma gabatar da su gaba kotu.

An baiwa shugaban wannan kamfani na Maslaha Motors kyakkyawar dama na ya je ya biya kudin harajin motoci sittin cikin shekara biyu guda hudu kacal ya biya, ya zo ya kwashe motoci ashirin da bakwai ba tare da izini ba, bayan wajen ya tashi daga karkashin kulawarsa ya dawo hannun hukumar kwastam har sai ya je ya biya dutin. Bai tsaya anan ba, sai dai ya yi karar hukumar kwastam ta kasa kotu na cewa an ci mutuncinsa da yancinsa, kuma sun je babbar kotun jiha, wadda ba ta da hurumin sauraren karar hukumar kwastam sai babbar kotu ta gwamnatin tarayya, duk da ba ta da hurumin ta ce a biya su wadansu kudi mu kuma mun daukaka kara a Kaduna.

Da yake Karin haske dalilin kai samamen da kwashe motoci ashirin, shugaban kwastam din ya bayyana dalilai kamar haka, an bashi damar ya je ya biya duti, tsawon shekara biyu cikin motoci sittin ya biya na mota hudu kadai. Na biyu idan aka rufe kamfani karkashi doka, kamar yadda muka yi masa, ya dawo karkashin kulawarmu hatta makullan suna hannun yan sandan kwastam ya je kuma ya bude har ya dauki motoci ashirin da bakwai. An zo daga helkwatarmu an yi bincike an kawo masu jimlar adadin da za su biya duk ya karya dokokin, akan wadannan helkwatarmu ta ga kamar akwai raina hukuma a ciki, cewar Dalha Wada Chedi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here