Advert
Home Sashen Hausa Dalilin Da Ya Sa Na Tsunduma Karatun Koyan Daukar Hoto A Wata...

Dalilin Da Ya Sa Na Tsunduma Karatun Koyan Daukar Hoto A Wata Jami’a Dake Kasar Burtaniya, Cewar Nafeesa Abdullahi (Kazar Hausa)

Fitacciyar jarumar Kannywood wanda ta shahara wajen fitowa a finafinai masu daukar hankali da nishadantarwa, Nafeesat Abdullahi ta bayyana cewa a kullum ita tana duba abinda zai amfanar da ita ne a rayuwa kuma hakan da take yi yana haifar mata da daukaka da ci gaba matuka.

Nafeesat ta shahara matuka a farfajiyar Kannywood wanda manazarta farfajiyar ke ganin tana daga cikin fitattun yan wasan da farfajiyar finafinan Hausa ta taba yi.

A hira da tayi da PREMIUM TIMES, jarumar ta bayyana dalilin da ya sa ta rungumi karatun koyon aikin daukan hoto wanda take yin sa a kasar Birtaniya.

” Daukan hotuna na daga cikin sana’a ta kuma ina matukar son daukar hotuna musamman na abubuwan ban sha’awa, abubuwa masu kayatarwa. Wannan shine dalilin da ya sa na rungumi daukan hoto da koyar da shi.

” Sannan kuma dalilin da ya sa ake yi mini ganin jaruma a Kannywood bai wuce maida hankali da na yi a sana’ata ba. Babu siddabaru ko wani abu da ban da ya kaini ga matsayin da nake. Maida hankali ne da kwazo da na saka shine kawai sirri na. Duk abinda na saka a gaba shi nake yi kuma nakan maida hankali ne matuka.

Bayan haka Jaruma Nafeesat ta ce yi karin haske game da matsalolin da farfajiyar Kannywood ta ke ciki ” Wannan ba sabon abu bane, matsaloli a farfajiyar fina-finai sukan bijiro a koda yaushe. Na mu aka sani, su ma sauran haka su kan yi fama da shi, ba a dai sani ne.

” Amma duk halin da aka shiga in shaAllahu za mu fito da karfin mu a Kannywood. Muna ma kokari domin farfajira ita take goya kanta, babu tallafi da take samu daga gwamnati.

Game da wadanda take jindadin fitowa a finafinai tare Nafeesat tace ba ta da wanda ya fi mata duk jarumin da ya iya taka rawa mai kyau a fim tana son taka wasa da shi ko ita a koda yaushe.

Sannan abinda yake birgeni a rayuwa shine idan naga yara kanan na yi mini lale-lale maraba suna farinciki da abinda na ke yi, abin na yi mini dadi matuka, yakan faranta mini rai sosai.

Akarshe ta yi magana kan kamfanin Tpumpy wanda ita jakadiyar Kamfanin ne.

” A dalilin wannan Kamfani, na mallaki kadarori sannan kuma duk shekara suna bani sabuwar mota da kuma kuma albashi a matsayina na jakadiyar Kamfanin.

Majiya: Premium Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: