Dalilin Da Ya Sa Na Mari Matar Obiano – Inji Bianca Odumegwu Ojukwu.

Daga Aliyu A Tsiga

Bianca, matar marigayi Odumegwu Ojukwu, ta bayyana dalilin da ya sa ta mari Ebele Obiano a wajen bikin rantsar da Farfesa Charles Soludo.

Bianca a wata hira da ta yi da tashar talabijin ta Arise TV a ranar Juma’a ta ce Ebele Obiano ba ta nan yayin da aka fara bikin ƙaddamarwar amma ta zo bayan sa’a guda da farawa.

Ta ce: “Ban kula da zuwanta ba. Da mamaki ta nufo ni ina tunanin za ta zo gaishe ni. A maimakon haka sai ta harare ni da muryarta ta ɗaga murya, tana yi min ba’a tana tambaya ta me zan yi, ta yi amfani da wasu munanan kalaman da ba a iya bugawa ba.

A cewarta, matar Obiano ta tambaye ta ko ta kasance a wajen bikin ne domin murnar ranar su ta ƙarshe a ofis. Na bar ta amma ta ci gaba da matsawa ta ɗora hannunta a kafaɗana tana ihu.

Yayin da na yi watsi da kalaman ta kamar yadda mutanen da ke zaune a kusa da ni suka ba ni shawara, na nemi sau biyu cewa ta daina taɓa ni da hannunta. Ta ci gaba da yin haka kuma ta yi ƙoƙarin taɓa kaina ta cire min ɗan kwali.

A lokacin ne na miƙe domin kare kaina na yi mata wani ƙazamin mari don hana ta kai min hari. Tana kaiwa nan na cire gashin kanta, sannan ta riƙe wig dinta da hannayenta biyu tana kokarin kwace min wig din.

Bianca ta kuma bayyana cewa yayin da mutane ke ƙoƙarin raba su, ta yi mamakin irin warin barasa da Ebelechukwu ke numfashi a daidai wannan rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here