Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami a ranar Laraba ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta wallafa sunayen masu daukar nauyin ta’addanci ba.

Ya ce gwamnatin Buhari ta dauki wannan mataki ne domin kada ta kawo tarnaki ga bincike.

Babban lauyan ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a New York, Amurka, a cikin wata sanarwa da Kakakin sa, Umar Gwandu, ya fitar ranar Laraba.

Malami yana mayar da martani ne kan sukar da jama’a ke yi wadda ta biyo bayan gazawar gwamnati na bayyana sunayen masu tallafawa ta’addanci a kasar.

Kwanan nan Hadaddiyar Daular Larabawa ta lissafa sunayen masu tallafa wa ayyukan ta’addanci 38, ciki har da ‘yan Najeriya shida.

Sanarwar ta karanta da cewa, “Lokaci bai cika ba na bayyana cikakkun bayanai.

“Babban abun nema yanzu shine cikar zaman lafiya da tsaro na ƙaunatacciyar ƙasarmu.

“Dangane da batun ta’addanci da kuɗi, mun yi nasarar gano waɗanda ake zargi da alhakin samar da kuɗin kuma mun toshe hanyoyin da ke da alaƙa da kudaden, yayin da muke gudanar da bincike mai zurfi wanda hakika yana tasiri sosai dangane da yaƙi da ta’addanci.

“Gaskiyar magana ita ce ana ci gaba da bincike kuma ana samun ci gaba. Saboda ana kan bincike, ba zan so magana ba dangane da yin bayanan da za su yi tasiri wajen lalata nasarorin da muke yi ba. ”

Daga karshe yace, cutar COVID-19 da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta yi ya shafi gurfanar da wadanda ake zargi da daukar nauyin ta’addancin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here