Wani dalibi da aka bayyana da Yahaya Aliyu wanda yake JSS 1 ya rasu ne, bayan da Malaminsu da aka bayyana da Gibson yayi masa duka da hannun bokiti.

Lamarin ya faru ne a Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Kwali a birnin tarayya Abuja. A ranar 9 ga watan Agustan da abin ya faru, Yahaya Aliyu ya tashi ba shi da lafiya, a haka yaje Makaranta a cewar abokansa, sai dai a ranar Malamin Mr. Gibson ya basu aikin gida inda ko wane dalibi ya bayar da nasa.

Da Malamin ya tambayi Yahaya Aliyu ko ina nasa aikin, sai ya shaidawa Malamin cewar baya jin dadi ne shi yasa bai yi ba. Daga bisani kuma Malamin ya dauki wani hannun bokiti ya kwakkwala masa a kansa, inda tundaga nan da ya zauna ya jingina kansa a gaban tebur, bayan dan lokaci kadan abokan Yahaya suka lura baya motsi.

Nan da nan suka sanar da Malamin, an garzaya da Yahaya Aliyu asibiti, amma tuni rai yayi halinsa. Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ASP Mariam Yusuf a tabbatar da faruwar wannan lamarin, tace Malamin yana tsare kuma suna kan bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here