Dalibar BUK da aka sace a jiya ta bulla a Sabongari

A joya Laraba aka bada sanarwar sace wata daliba Sakina Bello a unguwar Rijiyarzaki, akan hanyar ta ta komawa gida faga jami’ar Bayero, inda bayanai suka nuna anyi amfani da adaidaita aka sace ta.

Sai dai kuma anga dalibar a unguwar Sabongari fake yankin karamar hukumar Fagge a Kano. Dalibar dai ta bayyana cewar ta kubuto ne daga hannun mutanan da suka yi garkuwa da ita.

Dalibar dai tayi amfani da wayar salula ta kira dan uwanta inda ta bayyana masa cewar ta gudu daga hannun wadan da suka yi garkuwa da ita. Tun da farko dai mutanen sun bukaci a biya Naira Miliyan dari domin amsar fansar yarinyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here