Gwamnan jahar katsina Aminu Bello masari yaba dalibai (33) aiki, Kai tsaye wadanda suka fita da ajin farko a jami’ar Umyuk.

Shugaban hukumar kula da masu kwazo ta jahar katsina, Faisal Jafar Rafindadi, Ya bayyana hakan ranan juma’a da yamma a cibiyar yad’a labarai dake gidan gwamnatin jahar, a lokacin da yake tsokaci ga manema labarai akan abubuwan da aka cin mawa da Kuma Shirye-Shirye na babbar gasar masu kwazo dake tafe.

Daliban nan guda talatin da ukku (33) da suka samu aiki Kai tsaye a hukumar kula da ma’aikata ta jaha, sun had’a da duka daliban da Suka kammala da ajin farko a jami’ar cikin gida a tsakanin shekara ta 2020 zuwa 2021.

Rafindadi ya bayyana cewa hukuncin yazo ne domin shigar da sabbin jini a cikin hukumar kula da ma’aikata domin samun ingantaccen aiki.

Shugaban hukumar kula da masu kwazon ya shaida cewa jawo matasa acikin gwamnati na daga cikin kudurorin gwamnatin Masari, ya yabama gwamna Masari akan hangen nesa, dakuma Fadi tashin shi akan ganin cewa yakawo sabbin tsare tsare na saka gasa ‘kal’kashin hukumar kula da masu kwazo ta jaha.

Ya kuma cigaba da bayyana cewa babban ma’kasu din aiki na wannan hukuma shine bada ‘kwarin guiwa na kawo sauye sauye da Kuma cigaban masu kwazo, sannan kuma da karfafawa matasa gwuiwa na wannan jaha dakuma kasa baki daya.

A kashe ya sanar da cewa Wanda yazo a matakin farko a gasar masu kwazo zai samu kyauta ta naira 5million biyar, sannan Wanda yazo mataki na biyu zai samu 3million ukku, sannan kuma mataki na ukku zaisamu 1million daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here