NYSC ta ce da ga watan Janairu, 2022, sai waɗan da su ka yi cikakkiyar allurar rigakafin korona ne kaɗai za a baiwa damar yin rijistar zuwa bautar ƙasa.

“Da ga Janairun baɗi, sai waɗanda su ka nuna shaidar yin allurar rigakafin korona ne kaɗai za a bari su yi rijistar shiga sansanin ƴan bautar ƙasa.

“Mu ma son mu tabbatar da cewa muna ɗaukar matakan kariya daga cutar korona”, in ji Shugaban Hukumar, Birgediya-Janar Shuaibu Ibrahim, a yau Litinin a Abuja.

Ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke jawabi ga masu bautar ƙasa rukunin C, ayari na 2 ta yanar gizo.

Kakakin NYSC ɗin, Emeka Mgbemena, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Darakta-Janar din ya bada umarnin ne duba da ɓullar sabon nau’in korona na Omicron.

Shugaban ya ƙara da cewa ba za su yi lakwo-lakwo da biyayya ga matakan kariya daga kamuwa da korona ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here