DAGA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA. 

DAGA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA. 

DAGA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA. 

A Zaman Majalisar Dokokin na yau Laraba 14/101/2020. Wanda ya gudana a karkashin jagorancin kakakin majalisar Dokokin Rt Hon, Tasi’u Musa Mai Gari Zango. Yan majalisa guda  ukku ne suka gabatar da kudurorin su agaban Zauran majalisar domin cigaban Al’ummomin da suke wakilta.

kudiri na farko Shugaban masu rinjaye Dan majalisa Mai wakiltar karamar hukumar Rimi Hon. Abubakar Suleiman Abukur Kora’u ya Gabatar dashi, yana neman goyon bayan abokan aikinsa na Majalisa a tunatar da  majalisar zartarwa ta jihar Katsina,  Gina hanyar nan ta yar gamji, Eka, Sabon Gari, Shifdawa duk a cikin karamar hukumar ta Rimi. Gwamnatin data gabata ta aiwatar da fara aiki hanyar kashi talatin cikin dari , inda ya nemi wannan Gwamnatin ta kammala sauran aikin da kashi saba’in bisa dari. Hon. Abubakar Korau yana tunatar da majalisar data cigaba da kashi na biyu aikin, kashi na biyu shine zai isa Shifdawa yayi iyaka da karamar hukumar Bindawa.

A lokacin da yake Gabatar da kudirin  Hon. Abubakar Suleiman kora’u” Yace wata kungiya ce daga garin Alaraini suka zo Masa da wannan bukata. Kuma yayi alkawalin kawo wannan koke nasu a gaban zauran majalisa.

Kudiri na biyu, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar matazu Hon. Ibrahim U Dikko  shine ya Gabatar da shi. Inda yake rokon abokan aikinsa na majalisa dasu goya Mashi baya a turawa majalisar zartarwa ta Jihar Katsina.

Shima inda ya bukaci zauran majalisar daya    tunatar da bangaren zartarwa na jihar akan gyaran makarantar sakandire ta jeka kadawo ta mazoji ta karamar hukumar Matazu.

A lokacin da yake gabatar da kudirin Hon. Ibrahim U. Dikko “Yace Wannan shine karo na ukku,  yana kawo wannan kudirin gyaran wannan makaranta. “Ya Kara da cewa kimanin shekaru talatin da aka Gina wannan makaranta, bata taba samun gyaraba yadda ya dace. “Ya cigaba da cewa ya zuwa yanzu makarantar ta lalace matukar lalacewa,  hatta gidajen kwana na malamai dana Yan bautar kasa(NYSC) Wanda aka tanada domin su sun lalace. Sannan kuma makarantar tana bukatar zagayewa.

Sai dai bayan Gabatar da kudirin nashi, Kakakin majalisar ya bayar da umurni ga kwamitin ilimi na zauran majalisar daya zagaya domin duba halin da sauran makarantu a fadin jihar Katsina suke ciki na irin wannan Matsalar. Sannan su kawo rahoto a gaban zauran Majalisar domin daukar matakin daya dace.

Kudiri na ukku, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kusada Hon. Ghali Garba  Gidan Mutum Daya shine ya Gabatar da shi. ya roki abokan aikinsa na majalisa dasu goya Mashi baya a turawa majalisar zartarwa ta Jihar Katsina akan Gyaran makarantar firamare ta Tofa a karamar hukumar kusada domin Kara inganta harkar Ilimi a yankin.

A lokacin da yake gabatar da kudirin Hon Ghali Garba “yace yadda Gwamnatin jihar Katsina  kalkashin jagorancin Mai girma gwamna Rt Hon Aminu Bello Masari ta dauki bangaren ilimi da mahinmaci shiyasa ya kawo wannan kudirin domin taimakama Alummar yankinsa da yake wakilta.

Bayan tattaunawa da akayi kan wadan nan kudirorin, Daga karshe kakakin majalisar Dokokin ya umurci akawun majalisar (Clerk) a turance ya turama majalisar zartarwa domin aiwatarwa da wannan aikin na hanyoyin.

Abdurashid Musa

Camera Man/Reporter

Mobile Media Crew

October 14/2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here