Daga Abdullahi Aliyu ‘Yar’adua

Alkalai uku sun shigo a karkashin jagorancin Maishari’a Abbas Bawale.

Sauran wakilan Kotun sune Maishari’a Baraka Iliyasu Wali da Maishari’a Safiya Badamasi Umar, SAN.

An kira karar Mahadi Shehu da Mustapha Inuwa wadda aka daga zuwa yau don a soma sauraren korafin da Mahadi ya ce yana da shi game da sammancin da Babbar Kotun shari’ar Musulunçi ta biyu dake Katsina ta ba shi, a Abuja.

Sai dai kuma yau din ma, bayan Lauyan Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa, Barrister Abubakar Sahu Ibrahim ya mike ya gabatar da kan shi sai aka waiwayi bangaren Mahadi amma sai ba shi, kuma ba Lauyan shi; duk ba su zo kotu ba.

Anan ne sai Akawun Kotun ya shaida cewa Lauyan Mahadi, Barista Abbas Abdullahi Macika ya aiko da bukatar a daga masa saboda yana da wata Shari’ar yau, a gaban Kotun Tarayya dake Kano.

Da kotu ta nemi jin ta bakin Lauyan Mustapha Inuwa, sai ya ce ya amince daboda ya gabatar da takardar shedar cewa yana da Shari’a a Kano kuma Kotun ta Kano tana gaba da wannan saboda haka a ka’ida wajibi ne a daga masa.

Lauyan ya ce zama na gaba shi ne wanda zai kama 19 ga wata kuma ba zai yi masa daidai ba (ya kama daren salla) don haka ya nemi a kai su 26 ga wannan watan (Yuli) wanda zaman sai kasance a Daura.

Bayan sun tattauna, Alkalan Kotun sun amince da rokon Lauyan Mahadi sun daga zaman sauraren daukaka karar da Mahadin ya yi zuwa 26/7/2021, a garin Daura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here