Daga Fadar Sarkin Malaman Masarautar Gaya
Sheikh Dr. Yusuf Ali

Lahadi

28-08-1442/11-04-2021

Assalamualaikum Warahmatullah!

Mai Girma Sarkin Malaman Masarautar Gaya
Sheikh Dr. Yusuf Ali

Ya Wakilci Mai Martaba Sarkin Gaya Alh Ibrahim Abdulqadir (KIRMAU MAI GABAS)
Zuwa Wajan taron rufe Musabakar karatun Al-Qur’ani mai girma ta Gidan Radion Jahar Kano Wadda aka saba shiryawa sama da Shekaru Asharin da biyar a tsawon wadannan shekaru Mai girma Sarkin Malaman Masarautar Gaya Shine Alkalin Alkalai Na Wannan Musabakar.Amman a bana yazo a Babbar kujera ta wakilcin Mai Martaba Sarkin Gaya Uba a wannan taro kuma ya mika kyauta ga daliba mai hazaka da kokari wacce tazo ta biyu (2) a wannan musabakar wannan shekar sannan ya bada Gudunmowa ga masu shirya wannan Musabakar don kara karfafa musu gwiwa don cigaba da wannan muhimmin aiki na karatun Al-Qur’ani mai Girma

Taron ya samu halartar wakilcin Manyan Sarakunan. Kano, Bichi, Karaye da kuma Rano tare da hakimansu da manyan baki,Malamai, Alkalai, da kuma yan kasuwa da sauran jama’a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here