Daga Abuja:- ANYI ZANGA-ZANGAR BRING BACK OUR STUDENT.

-BYK-

Concern Nigerian tare da Ƙungiyar Ɗaliban Makarantar nan ta Gandun daji da ke Kaduna, tattare da iyayen ɗaliban da masu garkuwa da mutane suka sace, sun fito sunyi kira da a gaggauta ’yanto ɗaliban waɗanda ke cikin mawuyacin halin ko mutu ko rai. Kamar yadda masu garkuwa da mutanan suka faɗa yau Talata ne muddar da suka bada idan ba a bada kuɗaɗen fansa ba zasu kashe ɗaliban.

A hotunan za a ga ɗan rajin ‘yancin ɗan adam ɗinnan Adeyanju Deji a sahun masu zanga-zangar.

Shin ko gwamnatin taraiyya (Buhari) da ta jiha (El-rufa’i) zasu ji karɓi koken waɗannan mutane?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here