Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa, da yardar Allah, Gwamnatin shi ba za ta bar ma wadda za ta gaje bashin kudaden aje aikin ma’aikata ba.

Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne wajen bukin bude wani masabkin baki da kuma rukunin shaguna da kungiyar ma’aikatan lafiya reshen jihar Katsina ta gina a kan titin Goruba dake nan cikin birnin Katsina.

Alhaji Aminu Masari ya bayyana cewa a duk wata, gwamnati na kashe sama da Naira Miliyan Dubu Daya da Dari biyu (N1.2B) wajen biyan kudin fansho duk wata, kuma a kullum wannan kudi karuwa suke saboda karuwar masu aje aiki, ya kara da cewa yanzu haka shugaban ma’aikata na jiha ya turo mashi da takardar aje aiki (ritaya) ta Daraktoci guda ashirin (20) daga Ma’aikatar Ilimi ta jiha.

Gwamna Masari ya ankarar da shuwagabannin kwadago da ma’aikata cewa sabon tsarin tara kudin fansho na hada ka tsakanin gwamnati da Ma’aikata shi ne tsayayyen tsarin da zai kawar da duk wata barazana wajen biyan hakkokin wadanda suke aje aiki kan lokaci.

Ya kuma yaba wa shuwagabannin kungiyar ma’aikatan lafiyar a kan yadda suke sanya ya kamata wajen kashe kudaden da ma’aikatan suke tarawa.

A karshe ya kuma yi kira ga al’umma baki daya da kada mu gajiya wajen addu’o’in Allah Ya kawo mana dauki kan matsalolin da jiha da kasar ke ta fuskanta musamman na ta’addanci.

Daga: Abdulhadi Ahmad Bawa
___________________________________

Ya Allah Ka kawo karshen wannan ibtila’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here