Da Ni ɗan Siyasa ne, zan’iya bada maƙudan kuɗi ga ƙungiyar MOPPAN domin ta shirya film- Dr Muktar Al’ƙasim

Dr Muktari Al’ƙasim Malamin jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya yayi wannan Iƙrarin ne a wajen taron Shan Ruwa (IBTAR) da Haɗaɗɗiyar ƙungiyar shirya fina-finai ta ƙasa reshen jihar Katsina ta shirya domi sada Zumunci ga ‘ya’yan ƙungiyar.

Bayan jan hankali da nuna alaƙa ta ƙud-da ƙud da ƙungiyar take dashi ga al’uma ta hanyar faɗakarwa ilimantarwa da nishaɗantarwa, Dr Muktar yace; kungiya ce da take da saurin isar da sako kai tsaye ga al’uma ta hanyar wasan kwaikwayo kuma al’uma su fahimta su gane, yace; da ni ɗan siyasa ne da zan iya ware tun daga Miliyan ɗaya zuwa miliyan goma ga ƙungiyar domin su shirya Film akan abinda ya rataya akaina, na daga al’uma, “mi ya dace inyi minene haƙƙin kujerata dakuma su kansu al’uma mi yakamata suyi akan shuwagabanni” Inda yabada misali da shirin kwana Casa’in, na gidan Talabijin Arewa 24.

Dayake maida jawabi a wajen taron; Shugaban ƙungiyar na jihar katsina Comrade Lawal Rabe Lemoo, bayan nuna farin ciki da godiya ga manyan baki da ‘ya’yan kungiyar yace; “Irin wannan taron shine na farko a tarihin ƙungiyar tun bayan zuwanta a jihar katsina.

Taron yasamu baƙuncin shugaban hukumar KASROMA, da wakilcin shugaban gidan Talabijin na jihar katsina da ‘ya’yan kungiyar daga yankin Funtua da Daura dakuma cikin Birnin Katsina, inda ya gudana a tsohon gidan Gwamnatin jiha dake GRA. Anci ansha anyi Hani’an, angudanar da sallar Magriba cikin farinciki da mutunta juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here