A wata ganawa da yayi da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Dandume, mai neman takarar Kujerar Gwamnan jihar Katsina Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya koka akan yanda aka tsawwala kuɗin fom na tsayawa takarar Gwamnan, Inda yace “a jam’iyya adawa ace ana biyan kudin sayen Fom a kan kudi naira miliyan ashirin har da ɗaya wannan kamar an buɗe lasisin sata ne ga Gwamnoni,” yace idan aka hada waɗannan kudaɗen ga abinda yake ƙa’ada Al’bashin Gwamna ne na wata goma. Darma ya kara da cewa a shekarar dubu biyu da sha tara naira miliyan shida aka saida Fom, amma yanzu sun maida shi, miliyan ashirin da daya. “Munyi magana da wasu gingima gingiman ‘yan PDP a Abuj inda suma suka yimana korafi akan tsaar Fom din”.

A karshe Injiniya Muttaqa Rabe yace shidai kam bazai sayi Fom din takarar Gwamna ba, akai kasuwa. Ko da yake a cikin Faifan Bidiyo da Katsina City News tayi tozali dashi na ganawa da al’umar ta Dandume Injiniya yace masoya sun ce zasu saimashi Fom, saboda idan Allah ya bada Nasara Al’uma zasu amfanu da wadannan Ƙudurorin na injiniya, da kum samar wa matasa Aikin yi da koya masu sana’o,i fiye da yanda Cibiyar tasa take yi a yanzu, Inda shi kuma Injiniya yace zai ci gaba da neman mutane.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here