Da gaske an kai hari majalisar dokokin Jihar Imo?

BBC

Rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumuntar Najeriya na cewa, wasu bata gari sun kai hari kan majalisar dokokin jihar Imo da ke kudancin kasar.

Sai dai a wani bincike da BBC ta gudanar da gano cewa labarin ba gaskiya ba ne, bayan wakilin BBC a safiyar yau Litinin ya kai ziyara wajen ginin majalisar inda ya ce babu abin da ya same su.

Da yawa na tsammanin labarin gaskiya ne saboda yawan hare-haren da ake fuskanta na ‘yan kungiyar IPOB a jihar.

BBC

Ko a makon da ya gabata rahotanni daga Najeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun hari gidan gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma.

Jaridun Najeriya sun ce ƴan bindigar sun mamaye gidan gwamnan da ke Omuma a ƙaramar hukumar Oru ta gabas da safiyar Asabar.

Jaridar The Nationta ce ƴan bindigar sun kashe jami’an tsaro biyu da ke gadin gidan kafin suka cinna wuta

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here