DA DUMINSHI: Yaran Auwwalun Daudawa sun Kashe Tukur Mai Kyalla….

Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa an kashe biyu daga cikin manyan shugabannin ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a jihohin Zamfara da Katsina.

Auwalun Daudawa shi ne ya jagoranci ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar sakandaren Kankara ta jihar Katsina, ya kuma gamu da ajalinsa ne da yammacin juma’ar nan, sakamakon wata takaddama tsakaninsa da Tukur Mai Kyalla, wanda shi ma kwamandan wata runduna ce ta ‘yan bindiga a Dajin Gidan Jaja, da ke yankin karamar hukumar hukumar mulki ta Zurmi a jihar Zamfara.

Wata majiya daga dajin na Gidan Jaja, ta shaidawa Muryar Amurka cewa, Daudawa da yaransa sun saci shanun Tukur Mai Kyalla, wanda shi kuma ya ce lalle atabau sai an mayar musa da dabbobinsa.

To sai dai majiyar ta ce “Daudawa ya ki ya mayar da dabbobin na abokan sana’ar tasa, wadanda su kuma suka kai masa takakka, kuma Mai Kyalla ya sami sa’ar harbe Daudawa, inda shi kuma yaran Daudawa suka harbe shi.”

A cewar wasu rahotannin dai kazamin fada ne ya barke tsakanin gungun biyu na ‘yan bindiga, to sai dai duk da yake babu tabbacin ko rayuka nawa suka salwanta a fadan, to amma dai an tabbatar da mutuwar Daudawa.

Gwamnatin jihar ta Zamfara ma ta tabbatar aukuwar wannan lamarin, ta bakin kwamishinan lamurran tsaro Abubakar Dauran, wanda ya bayyana yakinin cewa “alhakin rantsuwa ne ya rutsa da Auwalun Daudawa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here