Da Duminsa HUK Poly za ta bude makaranta ranar 26 October
Hukumar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Katsina (Hassan Usman Katsina Polytechnic) za ta dawo gadan-gadan da karatu domin kammala zangon karatu na farko na shekarar 2019/2020
Kamar yadda Katsina Daily Post News ta ga takardar sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren kwalejin Nasir Danjuma BK ta nuna da an dawo za a ci gaba da kammala karatun zangon karatun na biyu sannan a yi jarabawa, kama Kuma da an gama jarabawar za a dosa zangon karatun na biyu