Advert
Home Sashen Hausa Da Dumi Duminta: Hukumar 'yan sandan Najeriya zata kori Abba Kyari, daga...

Da Dumi Duminta: Hukumar ‘yan sandan Najeriya zata kori Abba Kyari, daga aiki ~ Bincike

Wani bincike mai dauke da kwararan hujjoji daga majiyoyin hukumar ‘yan sanda ya bayyana yadda hukumar ‘yan sanda za ta iya sassautawa Abba Kyari.

Duk da sassaucin da zai samu, ana kyautata zaton za a iya korarsa daga aiki, amma ba lallai a mika shi ga kasar Amurka ba.

Akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa Abba Kyari dake fuskantar gurfana a Kotun Gundumar California ta Amurka bisa zarginsa da hannu a wata damfara ta shahararren dan damfara, Ramon Abbas (Hushpuppi), na iya samun sassaucin hukunci daga hukuma, kamar yadda Jaridar This Day ta ruwaito.

Abba Kyari, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban shugaban wata rundunar fikira ta IRT a Najeriya.

An dakatar da Abba Kyari yayin da aka fara gudanar bincike kan lamurran da suka faru tsakaninsa da Hushpuppi.

Bincike ya bayyana cewa, ana kyautata zaton Kyari ba zai dawo aikin dan sanda ba, amma zai iya samun sassaucin hukunci daga hukumomi, wanda daga cikin sassaucin shine; hukumar ‘yan sanda ba za ta mika shi ga hukumomin kasar Amurka ba.

Jaridar This Day ta tattaro cewa yayin da akwai kwararan alamu na cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda (IG) na iya bayar da shawarar a sauke Kyari daga mukamansa, Hukumar Kula PSC za ta zabi a sallamarsa gaba daya saboda girman laifin nuna rashin da’a ga aikin ‘yan sanda.

Majiya: Jaridar This Day

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: