Da Dumi-Duminsu: Masarautar Katsina Ta Dakatar Da Hakimin Ƙanƙara.

Masarautar Katsina ta fitar da sanarwar dakatar da Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Ƙanƙara Alhaji Yusuf Lawal Ƙanƙara.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana,dakatarwar ta fara aiki ne nan take daga yau Juma’a 30 ga watan Aprilu na shekarar 2021 har sai an kammala binchike akan laifinda ake tuhumarsa da shi.

Wannan dai sanarwa na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar Bello Mamman Ifo a Madadin Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here