Da dumi-dumi: ’yanbindiga sun kutsa kai cikin jami’a a Kaduna, sun sace dalibai

Rahotanni da DCL Hausa ke samu  sun bayyana cewa yanbindiga sun farmaki jami’ar Green Field mai matsugunni kan hanyar Abuja-Kaduna da ke jihar Kaduna tare da yin awon gaba da dalibai.

Jaridar DailyTrust ta  ce  yan bindigar sun farmaki jami’ar ne da misalin karfe 10 na daren ranar Talata bayan sun bindige maigadin makarantar tare da kwashe daliban da har yanzu ba a iya shaida yawansu ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar ASP Muhammad Jagile ya tabbatar da afkuwar lamarin, tare da shaida cewa duk da kai dauki da jami’ansu suka yi zuwa makarantar tare da hadin guiwar soji sun tarar har an tafi da daliban da kawo yanzu ba a san adadinsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here