Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa na ganin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a wani bangare na kokarin hana sauya shekarsa daga APC zuwa NNPP.

An ruwaito cewa, wannan gayyata ta Sanata Shekarau ta fito ne ta hannun gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Da farko dai an caccaki Gwamna Ganduje tare da yi masa ihu a lokacin da ya ziyarci gidan Malam Shekarau a Mundubawa don lallashinsa da ya bi shi su tafi Abuja a jirgin da zai je su gana da shugaban kasa a Abuja da karfe 1 na safiyar ranar Asabar.

Duk da cewa a baya Malam Shekarau ya amsa gayyatar da aka yi masa, amma makusanta Sanatan na cikin gida sun shaida cewa Malam Shekarau ya soke ziyarar ne bayan ya gano cewa ba shugaban kasa ne ke son ganinsa ba, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ne da wasu gwamnoni.

Mallam [Shekarau] ba a iya samunsa ta waya tun bayan da ya kammala shirin shiga NNPP. Don haka suna ta kokarin kai shi Abuja da lallashinsa ya ajiye shirinsa.

“Sun san Mallam yana mutunta hukuma, kuma ba zai yi watsi da gayyatar da shugaban kasa ya yi masa ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa suka kulla wannan shirin.

“Amma gaskiyar magana ita ce, Mallam ya kai makura. Idan ya yarda ya ci gaba da zama a APC, ina tabbatar muku kashi 80 cikin 100 na magoya bayansa za su koma NNPP.” Kamar yadda muka kalato daga Leadership Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here