Majalisar Wakilai a Najeriya za ta shirya halatta amfani da tabar wiwi a kasar domin amfanin tattalin arziki.

Kakakin Majalisar, Hon. Benjamin Okezie Kalu shine ya fadi hakan a lokacin taron manema labarai kan fa’idoji da damammakin da tabar wiwi ke samarwa a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kalu ya ce majalisar wakilai ta kammala shirin ta don shirya taron masu ruwa da tsaki na kwana biyu kan fa’idar tabar wiwi.

A cewarsa ranar da za’a gabatar da taron masu ruwa da tsaki, wanda zai ja hankalin mahalarta tsakanin masana kimiyya, kwararru a fannin likitanci da magunguna, manoma, kamfanonin inshora, shuwagabanni, da masu zuba hannun jari na kamfanoni masu zaman kansu an tsara su a ranakun 7 da 8 ga Yuni.

Ya yi bayanin cewa kasashe kamar Afirka ta Kudu wasu kuma a halin yanzu suna samun manyan kudaden shiga daga tabar wiwi wacce suke fitarwa zuwa wasu kasashen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here