DA DUMI-DUMI | Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci Barr. Muhuyi Magaji domin ya kare kansa.

Majalisar dokokin jihar Kano, ta bukaci dakataccen shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barr. Muhuyi Magaji Rimingado, da ya bayyana a gaban kwamitin dake binciken karar da aka kai a kansa.

Idan baku manta ba, majalisar dai ta dakatar da Muhuyi Magaji ne har na tsawon wata guda biyo bayan kin amincewa da Akawun da babban Akawu na jihar Kano ya aiko masa a hukumar Anti Kwaraption.

Takardar gayyatar wanda mataimakin darakta kuma sakataren kwamitin kula da harkokin shari’a, Abdullahi A. Bature ya sanyawa hannu a yau Litinin, ‘yan majalisar sun umurci Muhuyi Magaji Rimingado da ya gabatar da kan sa a zauren taron majalisar a ranar Laraba da karfe 12:00 na rana.

Majalisar ta kuma bukaci Muhuyi ya gabatar da bayanan asusun ajiyar sa na banki tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu tun kafin ranar Larabar.

Takardun da majalisar ta bukata a wajen Muhuyi Magaji sun hadar da dukkan bayanan bankunan sa da bayanan kudin da aka kashe a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da kuma asusun da ake turawa hukumar kudi tun daga shekarar 2015 zuwa yau.

Cikin takardun da ake bukata Muhuyi ya kawo akwai duk wasu fayal-fayal na kudaden da aka shigar a hukumar, takardun cikakkun bayanan abubuwan da aka maidowa hukumar daga shekarar 2015 zuwa yau; cikakkun bayanai na duk wadanda aka mayar musu da kayayyakin su da kuma bayanan gudummawa ko taimako ko tallafin da hukumar ta samu daga kamfanoni, daidaikun mutane, ma’aikatun gwamnati da kuma hukumomin gwamnati daga 2015 zuwa yau da sauran muhimman bayanai.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: