DA DUMI-DUMI: Boko Haram sun kai hare-hare kananan hukumomi 4 a jihar Bauchi sun lalata hanyoyin sadarwa
Daga Manuniya
Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da labarin cewa wasu yan bindiga da ake zargin Bako Haram ne sun kai hari a kananan hukumomi 4 na jihar Bauchi a yau Litinin.
Manuniya ta bayar da rahoton Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi (SSG) Alhaji Sabiu Baba, ya bayyana cewa hare-haren ya shafi kananan hukumomin Zaki, da Gamawa, da Darazo da kuma Dambam
Yan bindigar sun lalata karafunan sabis na waya da sauran abubuwa wanda ba a kammmala tantance barnar da sukayi ba ko adadin wadanda harin ya shafa.