Da Alamu Gwamnoni Sun Yiwa Shugaba Buhari Papalolo

Daga Abdulaziz, Abuja

A yammacin yau gwamnoni 22 na jam’iyyar APC mai mulki suka fitar da sunayen wadanɗa suke so su zame sababbin shugabannin jam’iyyar da za a zaɓa a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa yanzu haka a dandalin Eagle Square a Abuja.

Sai dai jerin sunayen ya yi nuni da cewa gwamnonin sun sa ƙafa sun shure buƙatar Buhari ta sanya wasu mutane a manyan guraben shugabanci a jam’iyyar.

A cikin mutane biyar da Shugaba Buhari ya gabatarwa gwamnonin mutum ɗaya ne suka amince da shi, wato shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu. Amma sun yi watsi da sauran huɗun.

Wannan alamu ne da ke nuna an kama hanyar jana’izar siyasar Buhari tun yana kan kujera–kodayake sakacinsa da watsi da al’amuran siyasa (kamar yadda yake nuna sakaci akan komai) shine abinda ya kai shi ga wannan ƙofar ragowa da gwamnonin jam’iyyar suke neman yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here