DA ƊUMI-ƊUMINSA: Mun Saka Lokacin Tsige Buhari Idan.…. – Ɗan Majalisa Ya Bayyana

Ɗan majalisar wakilai daga jihar Filato, Dachung Bagos ya bayyana cewa, idan matsalar tsaro ta cigaba da kazanta a watan Mayu to zasu tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ya bayyana cewa yanzu haka majalisar ta kafa wani kwamiti na mutane 40 da zai yi duba kan matsalar ta tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Sai dai yace tsige shugaban ƙasar shine mataki na ƙarshe da zasu ɗauka idan gwamnatin tarayya ta ƙi ɗaukar shawarar da zasu bata.

Ɗan majalisar ya bayyana haka ne ga tashar Channels TV kamar yanda Sahara Reports ta ruwaito. Yace babu ɗan majalisar da matsalar tsaron bata taɓashi ba kai tsaye ko ba ta kai tsaye ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here