DA ƊUMI-ƊUMINSA | Dangantaka Na Neman Yin Tsami Tsakanin Ƙasar Amurka Da Isra’ila Kan Faɗansu Da Falasdinawa
*Ji tambayar da Amurkar tawa Isra’ila
Ƙasar Isra’ila ta yi rugu-rugu da wani bene dake ɗauke da kamfanin dillancin labaran AP da Aljazeera da sauransu a zirin Gaza.
Hakan ya dauki hankalin Duniya.
Wannan dalili ne yasa a yanzu ƙasar Amurka ke neman Isra’ila ta mata bayanin dalilin ta na yin hakan, kamar yanda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito
A baya dai, shugaban ƙasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Hamas na ɓoye ne a cikin ginin kuma sun tabbata babu kowa a ciki kamin suka ruguza shi.