DA ƊUMI-ƊUMI | Gwamnatin Jahar Kano ta umarci ma’aikata su koma aiki. | ARTV KANO

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shi ne ya bayyana hakan ne a wata sanarwa a ranar Laraba.

Ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba da wannan umarnin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na mako-mako da ake gudanarwa a Afirka House dake Gidan Gwamnati, Kano.

Malam Garba Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan nasarorin da aka samu a yakin da ake yi da cutar ta COVID-19 a cikin watanni uku da suka gabata.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa manyan sakatarori da shugabannin sassan da hukumomi su isar da Wannan umarnin, da aka bayar don tabbatar da cewa ana bin ka’idoji da gwamnati ta sanya na kare yaduwar COVID-19 a wuraren ayyukansu.

Sanarwar ta Kuma ce Ma’aikata a Kano sun kasance a gida tun ranar 18 ga watan Janairu, biyo Bayan sake bullar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here