DA ƊUMI-ƊUMI: An ƙara tsawon wa’adin rufe layukan waɗanda basu da NIN

DA ƊUMI-ƊUMI: An ƙara tsawon wa’adin rufe layukan waɗanda basu da NIN

Hukumar NCC dake kula da kamfanonin sadarwa ta ƙara tsawon wa’adi da ta baiwa waɗanda ba su haɗa layukan wayarsu da lamar NIN ba.

A ranar 21 ga watan Disamban 2020 ne Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya bada umarnin ƙara wa’adin na mako biyu, inda da farko aka sanya ranar 29 ga watan Disamban a matsayin ranar da za a rufe layukan da babu Lambar NIN.

Hukumar NIMC dake yi wa ƴan ƙasa rijista ta fitar da sanarwar sake ƙara tsawon wa’adin da sati biyu daga 19 ga Janairu zuwa 9 ga watan Feburairu.

NIMC ta umarci ƴan kasa da basu yi katin shaidar zama ƴan ƙasa ba da su yi amfani da wannan dama domin yin rijistar.

A yau Talata 19 ga watan Janairu ne dai ake sa ran hukumar NCC za ta rufe layukan waɗanda basu bi umarninta na haɗa layukan su ba Lambarsu ta NIN kamar yadda ta rufe layukan da aka kasa yi musu rijista a shekarar bara.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: