CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Da yake amsa tambayan Manema Labarai, zan so na tabbatar wa dukkanin Ƴan kasa, kan su kore dukkan wani tsoro da mummunar fahimta kan lafiyar Allurar Rigakafi da aka gudanar da Sanyin Safiyar yau wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo SAN.

Bayan yayi Rigakafin, Shugaban kasa yaji babu wata matsala kana yaci gaba da gudanar da aikin sa. Idan da akwai wani Illar daya biyo baya daga bisani, ba zamu boye ba, to amma kawo yanzu babu wani Illa dake akwai na gaske ko cikin zuciyar Shugaban kasa. Yana cigaba da harkokin sa kamar kullum.

Muna fata wannan zai taimaka gurin aike sako mai karfi ga Mutane, Musamman wa’anda keda tarar-rabi da shakku kan rashin Illar Rigakafin.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
06 ga watan Maris, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here