Home Sashen Hausa Coronavirus: Za a yi wa Buhari da Osinbajo allurar riga-kafi

Coronavirus: Za a yi wa Buhari da Osinbajo allurar riga-kafi

Coronavirus: Za a yi wa Buhari da Osinbajo allurar riga-kafi

President Muhammadu Buhari and Vice-President Yemi Osinbajo

Shugaban hukumar ci gaban lafiya a matakin farko na Najeriya, Faisal Shuaib, ya bayyana cewa Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa, Yemi Osinbajo za su kasance cikin rukunin farko da za a yi wa riga-kafin korona na kamfanin Pfizer/BioNTech da ƙasar ta amince a yi amfani da shi.

Mista Shuaib ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin jawabin da kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa kan yaƙi da cutar korona.

Ana sa ran cewa zuwa ƙarshen watan Janairu wannan riga-kafin zai isa ƙasar kuma kusan guda 100,000 za su fara isa a karon farko.

Tuni dama kwamitin ya bayyana cewa ma’aikatan lafiya da ke kan gaba wurin yaƙi da cutar da tsofaffi masu shekaru ne za su fara amfana da wannan riga-kafin.

Baya ga Shugaba Buhari da mataimakinsa, akwai manya da ke cikin gwamnati irin su sakataren gwamnatin tarayya wato Boss Mustapha wanda yana cikin waɗanda za a yi wa riga-kafin domin mutane su gani kuma su yarda a yi musu.

Ya kuma yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa shugabanni za su zama na farko wurin karɓar wannan riga-kafin, inda ya ce ba ƙasar da ke so ta ga jogororinta korona ta kashe su.

Ya kuma bayyana cewa ko a wurin yaƙi, idan mutum yana so ya ga bayan maƙiyansa, abu na farko da yake yi shi ne kai hari ga shugabanni, da janarori, da an yi hakan, duka sauran sojojin jikin su zai mutu, in ji shi.

A cewarsa, domin gudun haka, ƙasar za ta bai wa shugabanninta a faɗin ƙasar wannan riga-kafin a karon farko domin kada a bar shugabannin ƙasar cikin hatsari.

Ya kuma bayyana cewa hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna wato NAFDAC, sai ta tantance riga-kafin tukuna a fara amfani da shi a ƙasar.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da annobar korona, Boss Mustapha, ya ce ganin yadda ake yawan samun ƙaruwar wannan cuta, ya zama dole mutane su ƙara taka tsan-tsan.

Shi ma ɗaya daga cikin masu jagorar wannan kwamiti, Sani Aliyu, ya bayyana cewa idan aka ci gaba da samun ƙaruwar masu kamauwa da wannan cuta ya zama tilas ga ƙasar ta sake saka dokar kulle.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Sake Gina Hanyar Katsina zuwa Kano: Ministan Ayyuka Mr. Fashola yace ana gab da kammala Aikin hanyar.

Sake Gina Hanyar Katsina zuwa Kano: Ministan Ayyuka Mr. Fashola yace ana gab da kammala Aikin hanyar. Ministan ya bayyana haka ne bayan zaman Majalisar...

An sanya dokar hana fita a garin Jangebe na Zamfara

An sanya dokar hana fita a garin Jangebe na Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a garin Jangebe...

Jama’atu Nasril Islam tace bazata Shiga Mahawar da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar da Maluman Kano ba….

Jama'atu Nasril Islam tace bazata Shiga Mahawar da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar da Maluman Kano ba.... A wata Sanarwa da Sakataren...

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da Bindiga Kirar AK-47

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da Bindiga Kirar AK-47 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa hukumomin tsaro umurnin bindige...

Ƙungiyar masu fataucin abinci zuwa kudancin ƙasar nan, Sun Amince Da Cigaba Da Kai kayan abinci Kudancin Nijeriya

Dillalan Abinci Sun Amince Da Cigaba Da Kai ka Ya Kudancin Nijeriya. Daga Comr Abba Sani Pantami Shugabannin dillalan Shanu da na Abinci a karkashin kungiyar...
%d bloggers like this: