SAKON TA’AZIYYA
Ina mika saƙon ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokan arziƙi na Ƙauran Katsina, Alhaji Nuhu Abdulƙadir, Hakimin Rimi, wanda ya rasu ranar Talata 23 ga watan Agusta 2023.
Ƙauran Katsina shugaba ne na kwarai marar misaltuwa, wanda ya gudanar da mulkin sa cikin himma da rikon amana. Jihar Katsina tayi rashin babban jigo kuma dattijo mai hangen nesa.
Allah ya jiƙan sa da rahama, ya gafarta masa kurakuren sa ya ba zuri’ar shi, Masarautar Katsina, da daukacin al’ummar Jihar Katsina kwarin gwiwar jure wannan babban rashi.
Sa Hannu:
Dikko Umaru Raɗɗa PhD.
Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyyar APC.
Source:
Gwagware Media Repoters
Via:
Zaharadeen Mziag
Previous Post