YAWAN SHAFUKA:. 194.
SHEKARAR BUGU: NAWUMBA 2021.
MAI SHARHI: DANJUMA KATSINA
A karon farko an buga littafi zuriyar Dallazawa, wanda Dallazawa suka rubuta da kan su. Marubutan sun yi amfani da rubutu da kuma rahotanni da aka taskace na tarihi. Kafin fitowar wannan littafin, tarihin ana samunsa ne gutsuttsure a littafan Tarihi daban-daban. Wasu bayanan kuma ana samun su ne a rahotanni Turawan mulkin-mallaka.
A karon farko wasu ’yan zuriyar Dallazawa sun dau lokaci suna bin littattafan da aka kawo tarihin Dallazawa da wasu littattafan da Malaman Jihadi suka rubuta suka kawo bayanan Dallazawa da kuma rahotanni da Turawan mulkin-mallaka suka rubuta suka yi nazarinsu, kuma suka tsamo bayanai inganattattu suka rubuta littattafin KATSINA GIDAN DALLAJE: TARIHIN ZURIYAR MALAM UMMARUN DALLAJE (DALLAZAWA 1700-1982). Dakta Aliyu Muri na Sashen Nazarin Tarihi a Jami’ar Ummaru Musa ’Yar Adua da ke Katsina ne Malamin Tarihi da ya yi aikin gyaran littafin kafin a kai ga buga shi. inda ya tabbatar duk bayanan da aka kawo sun cika mizanin tarihi.
Littafin ya kawo cikakkiyar wasikar USUL AL-SIYASA. Wasika wadda Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta wa Malam Ummarun Dallaje a kan ka’idojin shugabanci. Wannan shi ne karon farfko da aka fassara wasikar da Hausa. Wasika ce mai cike da ilmi, wadda a wannan lokacin da ake zamanin dimokaradiyya da zaben shugabanni, duk wani mai neman takara ko wanda ke kan mukami ya kamata ya karanta ta.
Littafin ya zo da wasu hotunan tarihi masu ma’ana da kuma tuna baya a kan tarihin Katsina da Gidan Sarautar Dallazawa, wanda aka ciro su daga dadaddun hotuna wanda wani dan gidan zuriyar ya dau shekaru yana tarawa.
Littafin an rubuta shi ne da harshen Hausa, domin manufar ya shiga lungu da sako da kuma saukin karatu ga kowa ba tare da neman sharhi ko bayani ba, wanda in da da wani harshe aka rubuta shi, wasu ne kawai za su iya karanta shi, sannan su fassara wa wadansu.
Bayan Sadaukarwa, Ta’aliki da kuma Godiya, littafin yana da babi har guda hudu. Babi na biyar Kammalawa ne da kuma Rataye. Kowane babi ya yi bayani filla-filla a kan abin da aka giina babi a kansa.
Bangon littafin zanen gidan Sarki ne, yadda yake tun zamanin Dallazawa da kuma wani dauke da tuta a kan doki. Bayan littafin kuma hotuna ne da bayan marubuta littafin.
Babi na farko na littafin takensa, Zuriyar Dallazawa a cikin jinsin Fulani. wanda ke dauke da duk bayanan tarihi da aka kawo na asalin zuriyyar Dallazawa. Da kuma tarihin asalin Fulani da suka samo asali daga jinsin Sahabin Manzon Allah (SAW) mai suna Ukuba bn Nafi (RA). Sannan suka kawo bayanan masana tarihi da rubutun da suka yi a kan asalin Dallazawa. Da kuma yadda Dallazawa suka zo garin Dallaje. Da asalin garin Dallaje. Duk a babi na daya daga shafi na 1-12.
Babi na biyu, wanda ya fara daga shafi na 13, ya karkare a shafi na 38 mai taken: Jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo. Yake-yaken Malama Ummarun Dallaje. Babin ya dauko tarihi tun kafin jihadin Dan Fodiyo da yadda suka hadu da Malam Ummarun Dallaje don neman ilmin addinin Musulunci. A wannan babin an kawo duk yake-yaken da Malam Ummarun Dallaje ya halarta har zuwa amso tuta don jihadi a Katsina. Har zuwa jihadin Katsina.
Babi na uku, wanda ya fara daga shafi na 39 zuwa na 101 mai taken: Kafuwar Daular Usmaniyya. Ya kawo bayanai da tarihin duk Sarakun Dallazawa a Daular Musulunci, wanda ya fara daga Malam Ummarun Dallaje (1807-1836). Saii Saddiku Ummarun Dallaje (1836-1844). Sai Muhammadu Bello Ummarun Dallaje (1844-1869). Sai Ahmadu Rufa’i dan Ummarun Dallaje (1869-1870). Sai Ibrahim dan Muhammadu Bello (1870-1882). Sai Malam Musa dan Ummarun Dallaje (1882-1887). Bayan rasuwarsa Abubakar dan Sarki Ibrahim ya gaje shi, wanda Turawa suka tarar a kan kujerar sarautar Amiril Mumuni.
A wannan babi marubutan sun yi wa tarihi adalci, inda duk wata matsala da aka samu ta gadon sarauta lokacin rasuwar kowane Sarki, sun kawo ta kamar yadda ta zo a tarihi. Duk matsalolin da Dallazawa suka fuskanta na yake-yake, zagon kasa da makida, duk sun kawo su. Hatta asalin farkon alakar Dallazawa da Sullubawa sun kawo shi ne lokacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Ummarun Dallaje, wanda ya jawo zuriyar Dahiru Kakan Muhammadu Dikko cikin fadar Sarkin Katsina.
Babi na hudu daga shafi na 101-164 shi ne babi mafi tsawo a littafin mai taken: Sarakunan Katsina Lokacin Turawan Mulkin-mallaka. Littafin ya kawo tarihin yadda Turawa suka shigo Katsina, suka iske Sarkin Katsina Abubakar yana sarauta.
Rubutun ya kawo yadda Sarkin Katsina ya wakilta Muhammadu Dikko ya wakilce shi a wajen Turawa. Ya kuma ba da tarahin Sarakuna Dallazawa da Turawa suka yi aiki da su . Na farko Abubakar dan Ibrahim 1887-1905. An kawo yadda aka cire shi daga mulki da yi masa gudun hijira sai Malam Yaro dan Malam Musa 1905-1906. Shi ma an kawo hawansa da yadda aka cire shi.
Daga shafi 125-154 an kawo labarin rayuwar Dallazawa ne a zamanin Sarkn Katsina Muhammadu Dikko.
Daga shafi na 155-164 an kawo yadda Usman Nagoggo ya zama Sarki da irin rawar da Yariman Katsina ya taka wajen daidaita biyayya ga sabon Sarki. Da yadda zumunci ya kara kyautata tsakanin Dallazawa da Sullubawa.
Babi na biyar daga shafi na 165-170 nazari ne a kan tarihin Katsina da ya kasu kashi uku, kafin jihadi, lokacin jihadi da zamanin Turawa da abin da ya biyo baya.
Rataye na daya bayani ne a kan sarautun da Dallazawa suke rike da ita a da. yanzu kuma ba ta a hannunsu. Rataye na biyu a fassarar usul siyasa ne cikakke. Rataye na uku kuma jerin sunayen ’ya’yan Ummarun Dallaje su 19.
A shafi na 193-194 jerin littattafai na tarihi da bincike wadanda aka dogara da su wajen nazari da binciken rubutun,.
An yi wa littafin bugu mai kyau da kuma tsanwar takarda. Littafin ya zo daidai lokacin bukatarsa. Wato zamanin da aka samu wasu shedanu suna shiga yanar gizo suna sukar jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo da kuma zuriyar Fulani baki daya.
DANJUMA.shine Mawallafin jaridun katsina city news,jaridar Taskar labarai da The links news.
@ www.katsinacitynews.com
@ www.thelinksnews.com
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08137777245
[email protected]