• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Monday, January 30, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Weekly Columns Rubutu da Marubuta

Ƙaddamar da yaƙin Neman zaɓen APC a Faskari Ƙalubalen da muka fuskanta II 

December 17, 2022
in Rubutu da Marubuta
0
Kungiyar da ke goyon baya da yaƙin neman zaben Tinubu ta “Dan Guruf Support for Tinubu 2023” ta shiga Mai’adua
0
SHARES
15
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 

Bayan da muka shiga But ɗin Motar a cikin takura, lokaci guda Kuma da farin cikin samun biyan buƙatar zuwa wajen taro a Kan lokaci (Duk da mun ɗan makara) cikin Ikon Allah muka isa garin Faskari karfe 11 da wasu Mintina, mun isa filin taro muka iske ba’a fara ba. Da gaske nidai kam naji dadi sosai ganin ba’afara taron ba. Saboda hakan zai bani damar Ji da ganin wainar da za’atoya a wajen daga farko har karshe. Ayyukan da na fara aiwatarwa da ni da abokan tafiya, shine abinda ya hau kan duk wani Danjarida alokacin da ya tsinci kansa cikin taro irin wannan. Babbar Sa’ar da nayi itace Babban mai Kaddamarwa wato Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari  bai zo da Wuri ba kasantuwar wasu dalilai, da suka sanya jinkirin hakan. Wannan shi ya bani damar barje gumi na da karantawa ko nazarin wannan gari da yayi kaurin suna wajen ‘Yan bindiga, (Masu garkuwa da mutane) A hankali filin taro ya zama babu masaka tsinke inda ya cika ya batse da Dan adam.Wajen karfe kamar biyu saura idan ban mantaba tawagar mai girma Gwamna ta iso, da sauran wadanda ake jira, taro yaci gaba. Na dauki abinda nake so naji abinda kunnena ya iya ji ga mahalarta taro musamman Gwamna Masari da Dantakara Dikko Radda. Ana cikin haka ne sai na tuna da cewa munzo fa filin taron ne bisa Maleji ma’ana, munzo a cikin Motar Aro, amma ta yaya zamu iya komawa gida? (Bisa tabi’a ta kawaici da Tunani idan mutum ya kyautata maka, to kada ka sake Neman ya ƙara idan har ba shi ya nema ba ko kuma babu wata mafita sai shi ɗin) shi yasa ma har na kasa sake cewa a matsa mu inda aka matso mu, don komawa koda inda aka daukemu da farko. Amma duk da haka Dan halas mutumin kirki sai da ya kira abokin tafiyata yace masa “Idan mun tashi tafiya muzo zasu tafi.” 

Rabon Wahala: 

A lokacin bama tare saboda mun rabu dasu da nufin zanje in dauko Jawabin Gwamna, a haka muka rabu, lokacin da ya kira, sai abokin tafiyata daga Katsina Breaking New yace masa “Ba yanzu zamu tafi ba su tafi.” Bansan anyi ba saida na zo yake fadimun yanda suka yi. Daga cikin Dajin da akayi taron Motoci ne Cunkushe har a kalla kilo mita shida zuwa 7 kuma duk wanda zaka gani cike take ko kuma neman abokan tafiyarsa da suka zo tare yake. 

Da naga tabbas akwai matsala (Duk da banyi niyyar sanarda maigidana matsalar da zamu fuskanta ba, amma dole na sanar dashi. Na kira Malam Danjuma Katsina na sanar dashi halin da ake ciki, ya nuna matukar Damuwa duba da yasan waje ne mai hatsari, a nan mukai ta bige-bigen waya domin neman mafita gashi amfara fita. Bankawo labarin bayan taro ba saboda takaitawa, amma dai Mimbarin taro ya balle mutane sun shiga razani, musamman wadanda suka rage a sama bayan tashi taron irinsu kwamishinoni da S.A da sauransu. Wani jami’in DSS ya nuna kwarewar aiki wajen fasa Kyamarar Abokin aiki na bisa zargin wai ana daukarsu Hoto, wanda kuma ba haka bane, kawai wani abu ne ya faru, sai shi abokina ya tsaya kallo wato kamar mai laifi ne aka kama, sai shi kuma abokina ya tsaya kallo da kyamara a hannunsa sai sukaga kamar daukarsu yake, nan take suka farfasa masa kyamara, kuma suka kwace Memory dake ciki, bayan bibiya da gudanar da irin nasu binciken da tabbatar da abinda suke zargi ba shi bane, suka bada Memory, amma barnar da sukai mana tabi shanun sarki. 

“Shima memory saida aka hadu a Katsina.” (Na danyi Ratse)Bayan tuntuba daga Mai gida da kuma samarmana mafita, Allah ya hukunta zamuyi tafiyar kasa zuwa inda muka fara samun mafita. “Kafin mubar wannan Daji Inaso inyi amfani da wannan rubutun inroki masu ruwa da tsaki akan sha’ananin tsaro cewa duk idan ta kama za’ai wani taro irin wannan, kuma a wajen da ake ganin yanada Barazanar tsaro, to bayan manyan baki sun bar wajen don Allah a hana jami’an tsaro ficewa subar Talakawa a wajen a dunga bari sai kowa ya fita su da ke da makamin kare kai su fita daga baya, amma gaskiya ambar mutane wajen babu jami’an tsaro sai ‘yan sojojin da dama nan suke.” Zanci gaba  Insha Allah.

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

Masari Ya Aurar Da Ya’yansa Maza Biyu A Katsina

Next Post

Ka San Haɗarin Ɗaga Yara Da Hannu?

Next Post
Ka San Haɗarin Ɗaga Yara Da Hannu?

Ka San Haɗarin Ɗaga Yara Da Hannu?

Recent Posts

  • APC ta gano kafafen yada labaran da PDP ke ɗaukar nauyi su yaɗa karya a kan Tinubu
  • Emefiele: We’ve collected N1.9trn old naira notes so far — N900bn more to go
  • Hanyoyi Shida Domin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi.
  • Bankin CBN Ya Samar Da Naira Miliyan 120 Domin Yin Canjin Kudi A Katsina.
  • INEC ta kara tsawaita wa’adin karbar katin zabe

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In