Physiology Hausa
A yayin ka zo kan mutum domin bayar da taimakon farko bayan afkuwar wani iftila’i kamar haɗarin abin-hawa, faɗuwa, faɗowa, ta’addanci ko rushewar gini sannan ka lura ya samu karaya a hannu ko ƙafa, to akwai matakai uku da ya kamata ka bi game da karayar kafin zuwa asibiti.
Matakan sune kamar haka:
- A tsayar da zubar jini idan buɗaɗɗiyar karaya ce. Buɗaɗɗiyar karaya ita ce karayar da ƙashi ya karye sannan ya fasa nama da fata har ya fito waje. Za a iya tsayar da zubar jini ta hanyar dannewa ko naɗewa da mayani ko ƙyalle mai tsabta. Kada a yi ƙoƙarin daidaita ƙashin da ya karye. Domin hakan na iya raunata jijiyoyin jini ko jijiyoyin laka da ke wurin.
- A tallafi karayar ta hanyar amfani da kara ko itace a gefe da gefe sannan a ɗaure domin hana karayar motsi.
- A sanya ƙanƙara tsawon minti 20 a wurin karayar domin rage kumburi, raɗaɗin ciwo da zubar jini. Ya kamata ƙanƙarar a farfasa ta sannan a ƙunshe ta cikin zani ko tawul mai tsabta. Kada a ɗora ƙanƙara kai tsaye a kan fata.
Da zarar an kammala ɗaukar waɗannan matakai uku, to lokacin garzayawa asibiti ya yi.
Source:
Physiology Hausa
Via:
Katsina City News